Skip to content

Yadda ake potato balls

Share |
Yadda ake potato balls
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

A yau za mu koyi yadda ake potato balls.

Abubuwan hadawa

  1. Dafaffen dankalin turawa
  2. Dafaffafen nama (ki daka shi)
  3. Dafaffafen kwai
  4. Tarugu
  5. Albasa
  6. Kayan Kamshi
  7. Maggi
  8. Garin biredi(bread crumbs)
  9. Filawa (ki dama ta da ruwa)

Yadda ake hadawa

  1. Dauko dafaffafen kwanki ki yanka shi (ko wani guda daya ki yankashi gida 6 zuwa 8) sai ki ajiye agefe.
  2. Dauko dakakken namanki ki sa a ciki sannan ki dauko dafaffafen dankalinki ki murtsika (za ki iya amfani da folk wajen murtsikawa) har sai ya baki kamar yanda ake yamballs.
  3. Sai ki dauko dakakken naman ki ki sa a cikin dankalin sannan ki kawo tarugu ,albasarki, kayan kamshi da gishiri kadan,maggi ki sa iya dandano da zai mi ki ki juya sosai har sai sun hade da juna sai ki shafa mai a tafin hannunki ki na diban hadin dankalin turawa, ki fadada shi sai ki kawo kwanki (wanda ki ka yanka a baya) ki sa a tsakiyan sai ki mulmula shi sosai. Haka za ki yi har sai kin gama da hadin dankalinki.
  4. Sannan ki dauko damemmiyar filawar ki na tsomawa a ciki ki na cirewa ki na sawa a garin biredi ki Haka za ki yi har sai kin gama sai ki daura man gyada akan wuta sai ki soya su kina tsanewa a matsani. Daga karshe ki dauko tsinken nama (skewers) ki sa a tsakiyan (amma ba dole ba ne ki sa tsinken ). A ci dadi lafiya.

Photo Credti: Chef Rodney

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×