Ku koyi yadda ake plantain sauce mai dadi ga kuma kyau. Wannan sauce na musamman yana da saukin hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya.
Abubuwan hadawa
- Agada (plantain)
- Dafaffen kifi (ki bare ki cire kaya)
- Albasa (ki yanka)
- Mai
- Tarugu (ki jajjaga)
- Kayan kamshi
- Maggi
- Lawashi (ki yanka)
Yadda ake Hadawa
- Ki dauko plantain na ki ki bare ki yanka shi kanana (irin yankan da ki ke so) sai ki barbada gishiri kadan. Ajiye a gefe.
- Sai ki daura mai kan wuta ki kawo plantain na ki, sai ki soya har sai ya soyu ki kwashe ki tsane a matsani. Ajiye a gefe.
- Rage man da ki ka yi suya dashi a wani kwano sai ki kara mai da kaskon kan wuta (ki bar iya mai da zai mi ki sauce na ki a ciki).
- Sai ki sa tarugu, da albasa, ki juya sannan ki kawo kayan kamshi ki sa, da maggi iya dandanon da zai miki ki sa sai ki juya.
- Kawo kifin ki ki sa ki juya, sai ki kara albasa a ciki ki juya.
- Sai ki rufe na dan wani lokaci (ki rage wuta sosai).
- Daga karshe, ki kawo soyayyar plantain na ki ki sa tare da lawashi ki sa ki juya ki rufe nadan wani lokaci.
- Sai ki kwashe a zuba a plate. Ana iya cin wannan sauce tare da alale (moimoi), ko shinkafa, ko taliya da dai sauransu. A ci dadi lafiya