Skip to content

Yadda ake peppered fish

Share |
yadda ake peppered fish
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake peppered fish na alfarma. Wannan hadin kifin din hadinne da ko agidan sarki, uwargida amarya ki ka yi za a sara miki.

Abubuwan hadawa

  1. Kifi (Ko wanne irin kifi danye)
  2. Tarugu
  3. Albasa
  4. Man gyada
  5. Maggi (dandanon da zai miki)
  6. Gishiri
  7. Koren wake
  8. Karas

Yadda ake hadawa

  1. Ki wanke kifinki ya wanku sosai da kyau tare da lemon tsami.
  2. Sai ki dauki gishiri ki barbada a kai, sannan ki sa a matsani ki barshi nadan wani lokaci.
  3. Idan ya tsane ba ruwa a jiki, sai ki daura kasko ki soya shi (ki tabbatar ishashshen mai ki ka sa yanda ba sai ki nata juya shi ba don yawan juyawa shi ne ya ke sa ya farfashe). In ya soyu ki sa a matsani ya tsane man jikinsa, sannan ki ajiye a gefe.
  4. Dauko tarugu da albasa ki gyara, ki wanke sai ki jajjaga, a ajiye a gefe.
  5. Sai ki daura tukunyanki akan wuta ki sa mai kadan ki yanka albasa ki soya sama sama, sai ki dauko jajjagen tarugu ki sa ki soya sama sama shima.
  6. Dauko kayan kamshi da curry da thyme da maggi (iya dandanon da zai miki) ki sa sai ki juya kidan soya sama sama nadan wani lokaci, anan sai ki sa ruwan zafi (Kamar cokalin cin shinkafa 4 misali idan ace kifin guda 2 ne) sai ki juya ki dauko kifin ki zuba a ciki sannan ki juya (ki tabbatar kayan miyan ki yaji a ko ina a jikin kifin).
  7. Sai ki dauko wata albasa ki yanka akai sai ki rufe shi na dan wani lokaci ya turaru har wannan ruwan ya tsotse, shi ke nan sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

Karin bayani 

Idan za ki sa su karas a ciki da su koren wake kuma sai ki gyara, ki yanka su. Ki sa musu ruwan zafi da baking powder ki rufe na dan wani lokaci sai ki tsane shi daga wannan ruwan ki kara wankewa da ruwa mai kyau sai ki tsane bayan kin kusa sauke kifinki sai ki zuba a ciki ki juya a hankali sai ki sauke.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×