Mu koyi yadda ake pasta jollof ga dadi ga kuma kyau. Wannan hadin pasta din na da saukin gaske wajen yi.
Abubuwan hadawa
- Taliya
- Macaroni
- Tarugu
- Albasa
- Peas
- Karas
- Lawashi
- Mai
- Maggi
- Gishiri
Yadda ake hadawa
- Daura tukunya babba akan wuta ki sa ruwa idan ya tafasa dauko taliya da macaroni ki sa gishiri kadan a ciki ki barshi nadan wani lokacin har sai ya yi rabin dahuwa sai ki kara ruwa ki tsane sa a matsani. Ajiye a gefe.
- Sake daura tukunya ki sa mai ki kawo albasa ki yanka ki soya sama sama sai ki kawo tarugu ki sa ki soya sama sama, ki sa maggi, da kayan kamshi, ki tsaida ruwa dai dai wanda zai karasa miki dahuwanki. Ki rufe ki barshi nadan wani lokacin.
- Sai ki kawo su taliyar ki zuba a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokacin har sai ruwan ciki ya shanye dauko karas, da peas ki sa ki barsu su turara sai ki sauke. A ci dadi lafiya.