Akwai hanyoyi da dama na sarrafa jollof rice, duk da cewa da yawan mutane musamman maza, su kan ce ba su son ta, sai dai da yawansu rashin son ya samo asali ne da rashin iya sarrafa ta. A yau na kawo maku hanya mai sauki kuma mai dadi, wadda idan kuka bi ta za ku ji dadi.
Abubuwan bukata:
1- 3 cups rice
2- 2 cups pepper mix (tattasai, tarugu, tumatur, albasa)
3- 1 sachet tomato paste
4- 6 cubes maggi and onga
5- 2 tablespoons margarine
6- 1 teaspoon ginger and garlic paste
7- 6 bay leaves
8- 1/2 cup oil
9- 1 teaspoon salt
10- 1 tablespoon jollof mix (Spicity and maggi)
11- 1 large carrot
12- 4 cups water (or as required)
13- 1 onion
Yadda ake yi:
1- ki zuba mai a cikin kyakkyawar non stick pot, sai ki saka ginger and garlic paste, ki saka albasa da bay leaves, ki saka tomato paste sannan ki soya sama sama da wuta kadan. Daga nan sai na kawo pepper mix wanda already na dafa su sannan na markada.

2- Sai ki zuba gishiri, seasoning, da kuma jollof mix dinki masu kamshi sannan wanda suke ja sosai saboda kalarta ta fita da kyau.

3- Bayan kamar minti biyar suna soyuwa, sai ki zuba wankakkiyar shinkafarki, ki zuba ruwa da diced carrots. Daga nan sai ki rufe ki bari ta dahu.

4- idan ta dahu sai ki bude ki saka margarine, ki rage wutar sosai. Bayan minti biyar sai ki bude. Ki yi serving da abin da kike so.

Idan kuna neman first class kayan kitchen, ku duba Bakandamiya shopping. Cikin rangwame da rahusa.