Ga yadda ake paratha mai jam a ciki mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne mai sauki da kuma dadi cikin ‘yan lokaci kadan uwargida za ki hada komai da komai.
Abubuwan hadawa
- Filawa kofi uku
- Jam
- Yeast cokali 2
- Mai cokali biyu
- Gishiri kadan
- Ruwan dumi
Yadda ake hadawa
- Da farko ki sami kofinki ki sa yeast na ki a ciki sai ki sa suga kadan (cokali daya) sai ki zuba ruwan dumi a ciki ki rufe shi nadan wani lokaci, za ki ga ya yi kumfa (yin hakan shi ne zai sa ki gane yeast na ki mai kyau ne ko ya baci).
- Ki tankade filawanki a kwano mai dan girma sai ki zuba gishiri kadan a ciki ki gauraya, sannan ki sa man gyada ki murja, sai ki dauko yeast na ki da ki ka jika ki zuba a ciki ki ta murza shi har sai ya hade jikansa (kwabin da za ki yi irin kwabin doughnut ko biredi za ki yi)
- Sai ki rufe ki kaishi rana kamar na minti arba’in don ya tashi.
- Sai ki dauko shi ki kara murza shi ki rufe shi, sai ki sami rolling pin (abun murza filawa) ko ki samu kwalban 7up na lemo. Sai ki sa filawa a kan teburi ko kuma tire sai ki murza shi har sai ya yi fale fale sai ki sami wani abu round ki sa akan (filawarki da ki ka murza tayi fale fale) sai ki yanka da wuka.
- Sai ki daura non stick pan akan wuta idan yayi zafi sai ki sa murzajjen filawarki ki gasa (idan ya fara yi za ki ga yana bubbles a jiki) sai ki juya dayan gefen shima ki gasa.
- Sai ki sami wani yadi mai kyau (kitchen towel) ki na sawa a ciki kuma ki na rufewa. Haka za ki yi har sai kin gama da sauran.
- Sai ki dauko parathanki ki shafa mishi jam kiyi nade kamar nadin tabarba (rolling). A ci dadi lafiya.