Skip to content

Yadda ake paratha

Share |
Yadda ake paratha
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ga yadda ake paratha mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne mai sauki da kuma dadi cikin ‘yan lokaci kadan uwargida za ki hada komai da komai.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi uku
  2. Yeast cokali biyu
  3. Mai cokali 2 (tsbp )
  4. Gishiri kadan
  5. Ruwan dumi

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki sami kofi ki sa yeast naki a ciki sai ki sa suga kadan (cokali 1) sai ki zuba ruwan dumi a ciki ki rufe shi nadan wani lokaci, za kiga ya yi kumfa (yin hakan shine zai sa ki gane yeast naki mai kyau ne ko ya baci).
  2. Ki tankade filawanki a kwano mai dan girma sai ki zuba gishiri kadan a ciki ki gauraya, sai ki sa man gyada ki murza, sannan ki dauko yeast naki da ki ka jika ki zuba a ciki ki ta murza shi har sai ya hade jikansa (kwabin da za ki yi irin kwabin doughnut ko bread za ki yi).
  3. Sai ki rufe ki kai shi rana ya sha rana kamar na minti arba’in don ya tashi. Bayan ya tashi, sai ki dauko shi ki kara murza shi ki rufe shi, sai ki sami abin murza filawa (rolling pin) ko ki samu kwalban 7up na lemo, ki sa filawa a kan teburi ko kuma tire sai ki murza shi har sai ya yi fale fale. Bayan haka, sai ki sami wani abu round ki sa akan (filawa ki da ki ka murza tayi fale fale) sai ki yanka da wuka.
  4. Ki daura tukunyar da baya kamawa (nonstick pan) akan wuta idan ya yi zafi sai ki sa filawa ki gasa (idan ya farayi za ki ga yana bubbles ajiki) sai ki juya dayan gefe shima ki gasa. Anan sai ki sami wani yadi mai kyau (kitchen towel) ki na sawa a ciki kina rufewa. Haka za ki yi har sai kin gama da sauran.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×