A cikin yanayin zafi, burin kowanne mutum shi ne ya samu abu mai sanyi ya jika makoshinsa. Shiyasa a yau muka kawo mukuyadda ake orange sunrise. Wannan mocktail din yana daya daga cikin abu mai dadi wanda za a ji dadinsa. Ga kuma azumi da muke cikinsa. Yana da saukin yi, sannan yana da saukin kashe kudi.
Abubuwan bukata
1- 1 bottle sprite
2- 20ml grenadine
3- 1 cup orange juice
4- 1 cup ice blocks
Yadda ake yi
1- Ki zuba orange juice, da kuma sprite a cikin glass cup.

2- Sai ki zuba kankara a ciki

3- Ki kawo sprite ki karasa cika cup din da shi.

4- Ki saka straw ki dan jujjuya shi.

5- Sai a yi serving chilled
