Ga wata hanya mai sauki mai dadi ta sarrafa naman kan rago. Za a iya ci haka nan ko da burodi, masa, ko dai abin da ake so.
Abubuwan bukata:
1- 1/2kg kan rago da kafafuwa
2- 2 tablespoons maggi and onga powder
3- 1 tablespoon mixed spices
4- 1/2 teaspoon curry powder
5- 1/2 sachet daddawa powder
6- 1/2 cup gyada
7- 1 cup pepper mix
8- 2 tablespoons oil
9- 1 tablespoon ginger and garlic paste
10- 1/2 onion
11- 1/2 teaspoon salt
Yadda ake yi:
1- Ki tafasa naman kai, sai ki wanke shi tas ki zubar da ruwan nan mai yauki. Sai ki dora non stick pot dinki mai kyau a wuta. Ki zuba mai, ginger and garlic, albasa, da kuma pepper mix.

2- sai ki zuba seasoning and spices, gishiri, curry, and daddawa. Ki soya har dai kamshi ya fara fitowa.

3- bayan ya soyu sai ki zuba gyada (za ki dan daddaka ta kadan ta fashe).

4- sai ki zuba tafasasshen naman kan nan wanda kika wanke. Ki zuba makimancin ruwa.

5- Bayan minti ashirin da biyar zuwa talatin (ko kuma sadda kika tabbata ya dahu) sai ki sauke.
