Moimoi ko in ce alala, tana daya daga cikin abincin gargajiya wanda suke gina jiki musamman da ya kasance ana amfani ne da wake wurin yin ta, kuma wake yana daga cikin protein. Ana iya yin ta da manja ko kuma mangyada. Sannan akwai zabin mutum ko ya yi da gwangwani ko leda, ko dai wasu moimoi containers da yake da su. Tana da saukin yi sannan tana da matukar dadi.
Abubuwan bukata:
1- wake gwangwani 4
2- manja rabin gwangwani
3- mangyada 1/4 gwangwani
4- 3 ajino moto
4- 1/2 teaspoon gishiri
5- 1/2 cup ruwan kanwa
6- 1/2 cup ruwan zafi (ko kuma gwargwadon ruwan da kullun alalar zai bukata)
7- 6 dafaffen kwai
8- 1 albasa mai lawashi
9- 4 tattasai
10- 6 tarugu
Yadda ake yi:
1- ki surfe wakenki ki wanke shi tas, ki cire hancin da kyau. Sai ki saka albasa, tattasai da attarugu ki markada a kyakkyawar blender ko kuma food processor.

2- ga shi nan bayan an markada. Ki nemi original bardefu blender a Bakandamiya Shopping ko food processor. Za su fi markada miki shi da kyau babu ruwanki da kaiwa engine balle a lalata miki markade a hada shi da gero ko dai wani abun da ba za ki so ba.

3- Sai ki zuba manja da mangyada a ciki

4- Sai ki zuba ruwan kanwa (yana hana alala ta yi saurin bata wa mutum ciki, sannan yana hana ta saurin lalacewa). Then ki kara da ruwa makimanci ko kuma yadda kike son kaurin alalarki.

5- ki zuba gishiri

6- sai ki saka farin magin ajino. In dai kina son alalarki ta yi danko sosai to kada ki saka wani magin again, duk wani magi da ya wuce fari to yana hana alala yin danko.

7- Sai ki buga komai ya hade

8- Daga nan sai ki samu gwangwanayen alala ko kuma moimoi containers wanda kike da su, ki shafe da manja, idan a leda za ki yi kuma ki zuba kullun kawai ki saka dafaffen kwai ki daure. A gefe guda kuma ki dora tukunya ko steamer a wuta da ruwa, idan ya tafasa sai ki jera moimoi din a ciki ki turara. Alala ta fi saurin dahuwa idan aka tsoma ta a ruwan zafi.
Idan ta dahu na minti talatin zuwa arba’in sai ki sauke ki yi serving da abin da kike so.
