Skip to content

Yadda ake miyar zogale

Share |
Yadda ake hada Miyar zogale
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

A yau za mu koyi yadda ake miyar zogale.

Abubuwan hadawa

  1. Zogale bushasshe
  2. Nama
  3. Maggi 5
  4. Albasa 1
  5. Attarugu 4
  6. Gyada (dai dai misali)
  7. Cittah
  8. Tafarnuwa

Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki wanke namanki kisa albasa da maggi ki dora a wuta ki tafasa
  2. Sai ki gyara zogalenki ki ajiye a gefe ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa da cittah ki a jiye a gefe.
  3. Sai ki duba namanki idan yayi saiki zuba jajageggen attarugun ki kara ruwa kisa maggi da gishiri dan kadan sai ki rufe yayi kamar minti biyar.
  4. Idan yayi sai ki zuba zogalen kirufe yayi minti biyar shima sai ki zuba gyadarki ki rufe.
  5. Idan ya nuna zakiji yana kamshi, sai ki sauke.
  6. Ana iya cin miyar zogale da tuwo kowa iri.

Photo credit: Chef Suad

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×