Miyar wake wata miya ce da yawa mafi akasrin yan arewa suke yin ta kuma suke cin sa. Miyar wake dai an fi alakanta shi ne da mutanen Niger , wato Nupawa kenan. Ana yin miyar ne da wanke, kifi busassa, daddawa, kayan miya , manja da sauran kayan dandano.
Ingredients
- wake
- manja
- spices( white pepper, chili pepper, onion powder)
- seasoning (maggi, royco, star)
- daddawa
- crayfish
Procedure
Wannan hadin na miyar wake, bata da yawa kuma ba wahala, sabida already ina da stew a ajiye wanda zan hada dashi.
Da farko, zaki jika waken ki na kusan 1 hour. Bayan nan sai ki surfa, ki wanke shi ya fita kal-kal babu bayan waken, kasa ko dutse.

Sannan ki zuba a tukunya da ruwa da dan gishiri kadan. Ko kuma kiyi blending din waken yadda nayi anan saboda yafi min sauri gaskiya.

Bayan nan sai ki daura manjan ki, ki zuba yankakken albasan ki, crayfish kadan, white pepper, maggi ko wani irin seasoning da onion powder dinki aciki, dan ya bashi taste mai dadi.

Next, sai ki juye daddawan ki da kika daka.

Bayan nan sai ki juye nikakken waken ki acikin manjan ki dan bari ya hadu for some minutes.

sai ki zuba crayfish dinki. Sannan idan kina so, zaki iya kara ruwa depending da yanda kika nika waken and if kina son shi da kauri ko da dan ruwa-ruwa.

Idan ya tafaso, shikenan miyar ki ta hadu.
Enjoy!