Ku karanta yadda ake miyar vegetable soup mai annashuwa da kayatarwa.
Abubuwan hadawa
- Alaiyaho
- Ganyen ugu
- Tarugu da albasan (a jajjaga)
- Maggi (iya dandanonki)
- Gishiri kadan
- Curry
- Kifi soyayye
- Dafaffafen naman (ki yanka shi Kanana )
- Man gyada
- Daffafen kifi (za ki cire kayan sai ki farfasa shi)
Yadda ake hadawa
- Ki gyara kuma ki yanka alaiyahonki da ganyen ugu naki sai ki tafasa ruwan zafi . Idan ruwanki ya tafasa sai ki ki zuba akai nadan wani lokaci (bawai za ki bari ya jima bane kawai yadanyi laushi ne)
- Ki tsane alaiyaho da ganyen ugun a matsami sai ki matse ruwan jiki ya fita, sai ki ajiyeye a gefe.
- Ki sa tukunyanki akan wuta ki sa man gyada kadan ki yanka albasa ki soya sama sama
- Ki kawo tarugunki ki sa a ciki, sannan ki dauko yankakken namanki ki sa a ciki shima ki soya sama sama
- Sai ki kawo kayan kamshi, curry ki sa a ciki ki kawo maggi ki sa (ya danganta da irin dandanonki) sai gishiri kadan sai ki juya
- Ki dauko soyayyen kifinki ki sa a ciki ki juya (idan zaki sa kifin da kika farfasa a anan ya kamata ki sa)
- Sai ki dan sa ruwa kadan ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin (ruwan kadan za kisa )
- Daga karshe kuma ki dauko ganyenki ki zuba a ciki, sai ki juya a hankali ki rufe tukunyanki yadan turara nadan wani lokaci sai ki sauke.