Ku koyi yadda ake miyar ugu ga dadi ga kuma kyau. Wannan miyar ugun gangariya ne dan gargajiya mai dauke da salon zamani.
Abubuwan hadawa
- Ganyen ugu (ki wanke, ki yanka)
- Karas (ki gyara, ki yanka)
- Lawashi (ki yanka)
- Tarugu (ki jajjaga)
- Tumatur (ki yanka)
- Albasa (ki yanka)
- Mai
- Kayan kamshi
- Maggi
Yadda ake hadawa
- Daura tukunya akan wuta ki sa mai ki kawo albasa ki sa, tarugu ki sa ki soya sama sama sannan ki kawo tumatur ki sa ki juya sai ki rufe nadan wani lokaci.
- Sai ki kawo kayan kamshi, da maggi iya dandanon da zai miki sannan ki sa, da gishiri kadan ki sa, ki juya sannan ki kawo ganyen ugu ki sa dana lawashi ki juya ki rufe nadan wani lokaci.
- Daga karshe ki kawo karas na ki ki sa a ciki ki rufe yadan turara sai ki sauke ki zuba akan abinci. Ana iya cin wanann miyar da tuwo ko wani iri ne ko shinkafa ko couscous da dai sauran su. A ci dadi lafiya.