Skip to content

Yadda ake miyar kwai

Share |
Miyar kwai
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ga yadda ake miyar kwai gangariya cikin sauki.

Abubuwan hadawa

  1. Kwai
  2. Tarugu
  3. Albasa
  4. Curry da thyme
  5. Garin citta kadan
  6. Koren tattasai
  7. Koren wake
  8. Karas
  9. Butter
  10. Knor chicken ko maggi chicken (ya danganta da irin dandanon ki)

Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki fasa kwanki a ciki wani karamin kwano, sai ki yanka albasa a ciki, ki ajiye a gefe.
  2. Ki wanke ki cire dattin bayan carrots naki, ki wanke su Koren wake ,albasa dasu tarugunki, sai ki yanka su dogo dogo, bayan kin gama dauko carrot naki da koren wake, ki sa masa ruwan zafi sosai (tafasashshe), sai ki sa baking powder Ko kanwa a ciki ki rufe shi nadan wani lokaci, sai ki cire shi cikin ruwan sannan ki sake wanke shi ki tsane shi, sannan ki ajiye a gefe.
  3. Daura tukunyarki akan wuta ki sa butter kadan ki narka, sai ki kawo albasarki ki yanka a ciki ki soya sama sama.
  4. Dauko yankakken tarugunki ki sa a ciki da su maggi , garin citta kadan, curry da thyme sai ki kawo ruwan zafi kadan sai ki juya ki rufe shi na dan wani lokaci.
  5. Sai ki dauko kwanki (wanda ki ka fasa a kwano) ki zuba cikin tukunya ki dake kan wuta ki rufe ki barshi nadan wani lokaci.
  6. ki rage wuta sai ki bude ki kawo su carrot, koren wake ki sa sai ki juya shi a hankali ki kara rufeshi nadan wani lokaci har sai ruwan ciki ya shanye, sai ki sauke

Za ki iya ci da soyayyen dankalin turawa ko doya. 

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

4 thoughts on “Yadda ake miyar kwai”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×