Ku koyi yadda ake miyar kuka ‘yar Borno ga dadi ga kuma kyau. Wannan miyar kuka ta musamman ce, ba irin miyar kuka ce da kuka sani ba.
Abubuwan hadawa
- Garin kuka
- Tafarnuwa
- Citta
- Nama gadon baya
- Tattasai da attarugu kadan
- Maggi
- Albasa
Yadda ake hadawa
- Ki yanka albasa ki dan soya sama sama ki sa nama a ciki da kayan kamshi da ruwa naman ya yi ta tafasa har ya dahu
- In ya dahu a tsame naman a daka a mai da shi cikin ruwan sa da ke kan wuta.
- Sai a yi jajjagen tarugu da tattasai da tafarnuwa da citta a zuba a ciki.
- A sa maggi a bari ya tafaso sai a kawo kuka a rika kadawa a hankali har ya yi kauri.
To sunan wannan miyar manta sunan ka. Mu dai ‘yan Borno da biski muke ci. Amma za a iya ci da kowani irin tuwo. Ni dai biski shi ne zabi Na. Sannan za a iya karanta: Lemon cucumber drink sauransu.
Zan bibiyi wannan Miya Amma bana fata na manta komai🤣🤣🤣🤣🤣
Ina fatan tayi dadi