A yau za mu koyi yadda ake miyar koda.
Abubuwan hadawa
- Koda daidai bukata
- Maggi 5
- Albasa 1
- Attarugu 4
- Cittah 2
- Tafarnuwa 3
- Kori
Yadda ake hadawa
- Da farko zaki wanke kodarki ki yanka kisa a tukunya, ki yanka albasa ki sa gishiri kadan, da maggi daya ki dora a wuta.
- Idan ya tafasa sai ki daka attarugu da albasa da tafarnuwa ki zuba ki sa cittah ki zuba ruwa ba mai yawaba sai ki rufe.
- Idan ya dafu, za ki ji gida ya game da kamshi.
Photo Credit: Shutterstock.com