Ku koyi yadda ake miyar hanta. Wannan miyar hanta din yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya.
Abubuwan hadawa
- Hanta rabin kilo
- Attarugu 4
- Tattasai 3
- Albasa 2
- Maggi 5
- Gishiri
- Citta 3
- Tafarnuwa 2
- Kori (Curry)
- Onga
- Man girki
Yanda ake hadawa
- Da farko dai uwargida zaki wanke hantar kiyanka daidai misali
- Saiki sa a tukunyarki ki yanka albasa, kuma ki sanya maggi kwaya daya da dan gishiri
- Idan yayi sai ki sauke ki kwashe a wani kwano, sai ki zuba mai da kayan miyanki ki soya ya soyu da kyau
- Idan ya soyu sai ki zuba ruwa kadan ki sa hantar ki kawo maggi, da gishiri, da citta, da tafarnuwa, da kori ki sanya
- Sai ki barshi kamar minti shabiyar zaki ji gida yadau kamshi sai ki sauke