Mu koyi yadda ake miyar egusi cikin matakai shida. Wannan miyar egusi dai miya ne sosai mai kyau da kuma dadi da kuma saukin bi.
Abubuwan hadawa
- Egusi (ki nika)
- Dafaffafiyar ganda
- Stock fish (ki jika da ruwan zafi)
- Dafaffafen kifi (titus)
- Manja
- Ganyen ugu
- Tarugu (ki jajjaga)
- Albasa (ki yanka)
- Tumatur (ki yanka kanana)
- Maggi
- Kayan kamshi
Yadda ake hadawa
- Ki sami kwano babba ki zuba garin egusinki a ciki sai ki zuba mishi ruwa akai (ruwan kadan za ki sa) sai ki sa cokali ki dama(kaurin sa ya zama kamar kullin kosai) ajiye a gefe.
- Daura tukunya ki akan wuta ki sa manja ki zuba albasarki a ciki ki soya sama sama.
- Sai ki kawo egusi ki na diba da cokali ki na zubawa a cikin manjan ki na kan wuta sai ki barshi na dan wani lokacin, sai ki juya ki rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan.
- Dauko tarugu ki sa ki juya sama sama sai ki kawo tumatur da albasa (wanda ki ka yanka) ki sa a ciki ki juya, ki kawo kayan kamshi, maggi (iya dandano da zai miki) ki sa a ciki ki juya.
- Dauko ruwan dumi ko na zafi ki sa( ruwan dan dai dai kadan za ki sa) ki juya ki rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan har sai ruwan ya ragu.
- Daga karshe sai ki kawo ganyen curry da ganyen ugu ki sa ki juya ki rufe tukunya ki na dan wani lokacin sai ki sauke.
Nice
Wow nice