Skip to content

Yadda ake miyar egusi

Share |
Yadda ake miyar egusi
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ga yadda ake miyar egusi mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne mai sauki da kuma dadi cikin ‘yan lokaci kadan uwargida za ki hada wannan miyar.

Abubuwan hadawa

  1. Egusi ( Nikakke)
  2. Ganye Ugu (ki wanke, ki yanka)
  3. Alaiyaho (ki gyara ki yanka, a wanke)
  4. Stock fish
  5. Kwai
  6. Tarugu
  7. Albasa (a jajjaga)
  8. Kifi banda
  9. Nama (soyayye)
  10. Maggi
  11. Curry
  12. Gishiri
  13. Kayan kamshi
  14. Manja da mangyada

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko egusi ki diga mishi ruwa kadan ki sa a turmi ki daka (za ki ga yana hade jikansa har mai na fita ajikinsa) idan kin gama sai ki dinga dibanshi kina mulmula shi Kamar (karago) haka za ki yi har sai kin gama.
  2. Sai ki fasa kwanki ki sa albasa ki kadashi sosai ki ajiye a gefe shima.
  3. Ki dauko kifinki ki cire kayan sai ki jika shi da ruwan zafi, sannan haka stock fish shima ki jika shi da ruwan zafi (ko ki daura kan wuta ki tafasa har yayi laushi).
  4. Sa tukunyanki akan wuta ki sa mangyada da manja ki yanka albasa ki soya sama sama.
  5. Ki dauko tarugu da albasanki ki sa a ciki ki soya sama sama, sai ki kawo kayan kamshi, gishiri da maggi (iya dandanon da zai mi ki).
  6. Ki dauko kwanki ki sa a ciki ki rufe tukunya ki ki rage wutan ki barshi nadan wani lokaci sai ki bude ki juya shi sai ki sauke ki ajiye a gefe.
  7. Ki daura wata tukunyanki akan wuta ki sa ruwa (ruwan kadan za ki sa) idan yayi zafi ya tafasa sai ki dauko egusi ki(da kika mulmula) ki sa a ciki ki rufe, ki barshi nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye.
  8. Sai ki dauko tukunyanki (Wanda Ki ka yi shi kamar sauce na kwai) ki kawo egusi da kika dafa ki juye ki kawo su kifinki ki sa a ciki dasu soyayyen nama ki sa dasu sauran kifi banda (wanda Ki ka gyara shi), sai ki Rufe tukunya nadan wani lokaci.
  9. Sai ki dauko alaiyaho da ganyen ugu naki ki sa a ciki ki rufe ki barsu su dan turara sai ki sauke.

Ana iya ci da tuwon shinkafa, sakwara, tuwon masara da dai sauransu. A ci dadi lafiya

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×