Mu koyi yadda ake mixed fruits juice cikin sauki, abubuwan hadawa guda tara, ta hanyar bin matakai guda shida kacal.
Abubuwan hadawa
- Kankana (yanka irin na naira100)
- Apple 1
- Abarba (yanka irin na naira 100)
- Mangoro 1
- Lemon zaki 2
- Lemon tsami ½ (ba dole bane)
- Foster clerk ko sugar (yanda zakin zai miki )
- Danyar citta 1(karama)
- Kaninfari gudu uku
Yadda ake hadawa
- ki gyara kankananki, ki cire wannan koren bayan sai ki yanka ta kanana kina cire bakaken kwallayen da ke ciki sai ki ajiye gefe.
- Ki dauko mangoro ki fere bayan (fatan bayan) sai ki yanka kanana ki cire kwallon tsakiya, ajiye a gefe.
- Haka lemon zaki shima fere bawon bayan ki yanka shi kanana, sai ki dauko danyar citta ki cire dattin bayan ki yanka kanana, ajiye a gefe.
- Sai ki dauko apple naki shima ki yanka shi kanana ajiye a gefe.
- Dauko blender ki dauko duka kayan da ki ka yanka a baya, ki zuba a cikin blender, sai ki jefa kaninfari a ciki ki sa ruwa kadan a ciki ki markada har sai kinga ya yi laushi.
- Sai ki juye a wani kwano babba ki kara masa ruwan sanyi sosai ki tace sai ki zuba suga ko foster clerk kadan (iya zakin da zai mi ki) sai ki sa a jug ko ki kara mai da shi fridge dan yakara sanyi. A sha dadi lafiya.