In dai kina so ki iya hadadden milk cake (tres leches) to a yau na zo maku da shi. Babu inda ba za ki shiga ba da wannan recipe din.
Abubuwan bukata:
For the cake:
1- 4 eggs
2- 3/4 cup flour
3- 3/4 cup sugar
4- 1 teaspoon vanilla flavor
For the milk mixture
1- 1 cup powdered milk
2- 1/2 cup peak milk
3- 1/2 cup whipping cream
4- 1 hollandia full cream
5- 1/2 tin evaporated milk
6- 1 and 1/2 cup cold water
7- 2/3 cup condensed milk
For the topping
1- 1 cup whipping cream
2- 1 cup cold water
3- 4 oreos biscuits
4- 2 biscuff
5- 2 tablespoons powdered milk
6- 4 tablespoons caramel sauce
7- 2 tablespoons chocolate chips
Yadda ake yi:
1- ki zuba kwai a cikin mixer, sai ki saka sugar da flavor ki ta mixing sosai har sai sugar ya yi kumfa sannan ya kara yawa.

2- sai ki dinga zuba flour a hankali har sai ta kare duka. Sannan komai ya hade.

3- ki samu pan ki saka baking paper, sannan ki juye batter din a ciki. Ki gasa na minti talatin, wutar za ta zama medium, kuma da wutar kasa kadai ake gasawa.

4- idan ya huce sai ki yanka shi daidai girman robobin da za ki amfani da su.

5- ki zuba madara, whipping cream, da condensed milk sai ruwa a cikin bowl.

6- ki zuba hollandia da madarar ruwa a ciki ki motsa.

7- ki zuba whipping cream da ruwan sanyi a bowl ki ta mixing har sai ya zama haka.

8- ki dinga dibar wannan hadin madarar kina zubawa a cikin cake har sai duka ta kare. Sai ki zuba whipping cream a cikin piping bag, ki piping dinsa yadda kike so.

9- then Ki topping da abin da kike so.

10- ki saka a fridge ya yi sanyi sannan ki sayar ko ki serving.
