Ku koyi yadda ake meatballs. Wannan meatballs ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!
Abubuwan hadawa
- Minced meat (nikakkiyar nama)
- Tafarnuwa
- Albasa (zaki yanka ta kanana)
- Gurzarjiyar ginger
- Gishiri
- Maggi
- Kwai
- Attarugu
- Masoro
- Corn flour
Yadda ake hadawa
- Ki samu roba ki saka nikakkiyar nama, albasa, attarugu, ginger, tafarnuwa, kwai, masoro (za ki dake ta).
- Sai ki kwaba ki mulmula ya zama ball, ki samu corn flour ki saka a wani roba sai ki saka meat balls din a ciki ki yi rolling corn flour ta kama jikin namar.
- Sai ki daura mai a pan in ya danyi zafi ki zuba ki soya.
Karin bayani
Kada ki cika wuta sosai yayin suyan.