Ku koyi yadda ake meat pie mai ban sha’awa ga dadi ga kuma kyau. Wannan gangariyar meat pie idan uwargida ta gwada zata bamu labari!
Abubuwan hadawa
- Filawa
- Butter
- Salt
- Baking powder
- Dafaffen nama
- Dankali turawa (ki dafa shi)
- karas (ki gurza shi)
- Maggi
- Kayan kamshi
- Mai kadan
- Albasa
- Tarugu
- Kabeji
Yadda ake hadawa
Dought
- Ki samu bowl ki sa filawa sai ki sa butter ko man gyada sai ki samu egg ki sa ki kwaba sosai.
- Sai ki sa ruwan (ruwan dai-dai yadda zai karasa kwaba miki filawar ki) sai ki kwaba shi sosai. Ba a so ya yi ruwa-ruwa, ya yi dai-dai yadda za a iya murza shi a sa filling. Ki ajiye a gefe.
Filling
- Ki samu nama ki tafasa ki yanka ko ki daka sai ki daura pan na ki a kan wuta ki kawo naman ki, ki jajjaga attarugu da albasa, mai kadan sai ki dauko dankali (dama kin yanka su kanana) da su karas shima ki hada ki sa.
- Ki kawo kayan kamshi, maggi gishiri kadan daga ki sa.
- Daga karshi ki kawo kabeji ki sa sai ki juya ki dan soya su sama-sama sai ki ajiye a gefe.
- Ki dauko kwabin filawarki ki murza da abun murza filawa ya yi fadi (ki yanka shi da dan fadi ya baki 4 corners) sai ki zuba fillings
- dinki ki rufe ki samu folk ki danna bakin din (edge) sai ki soya a mai. A ci dadi lafiya.