Akwai hanyoyi da dama da ake bi wurin sarrafa masa. A yau na zo maku da wata sabuwar hanya da na tabbatar ba kowa ne ya san ta ba.
Abubuwan bukata:
1- 4 cups farar shinkafar tuwo
2- 1/4 cup surfaffen waken soya
3- 1 tablespoon yeast
4- 1/4 cup sugar
5- 1 tablespoon salt
6- 1 large onion
7- 1 cup oil for frying
Yadda ake yi:
1- Ki jika shinkafa awa shida ko kuma da dare zuwa safiya. Sai ki wanke ki tsame daga ruwa. Ki zuba gishiri, sugar, waken soya (wanda kika surfe), albasa, sai yeast.

2- Sai ki kai a markada. Ko kuma ki amfani da original blender daga Bakandamiya shopping. Mai kyau wadda take markada komai.

3- Sai ki debi kadan ki dama kunu. Sannan ki juye a ciki.

4- Daga nan sai ki lullube shi ruf ki ajiye a wuri mai dumi. Zuwa minti arba’in ko awa daya ya tashi.

5- Sai ki dora masa pan dinki a kan wuta ki zuba mai. Idan ya yi zafi sai ki zuba kullun masar. Idan kina soya masa kika ga ba ta yin wannan duhun to ki dan zuba sugar makimanci shi zai sa ta yi kalar haka.

6- Daga nan sai ki serving da abin da kike so. A nan na yi serving ne da kuli-kuli

7- Nan kuma na yi serving da naman kai.
