Akwai hanyoyi da dama na sarrafa awara. Na san kai tsaye idan na ce masar awara za ku yi mamakin ta yaya za a sarrafa awara har a yi masarta? To ga amsarku. Kuma hanya ce sassauka, ga dadi. Na tabbata idan kuka gwada sau daya za ku ci gaba da yi.
Abubuwan bukata:
1- 20 pieces awara
2- 5 attarugu
3- 1 albasa mai lawashi
4- 1 tablespoon maggi powder
5- 1 teaspoon salt
6- 1/2 cup oil
7- 1/2 teaspoon curry powder
8- 4 eggs
Yadda ake yi:
1- ki zuba awararki a cikin food processor ko kuma blender. Ko ki mashing da spoon ko masher ko dai wani abu da zai sa ta niku da kyau.
2- Ki zuba attarugu da albasa

3- Sai ki dauka ki nika.
4- Ga shi nan bayan na nika. Haka ake son ta kasance, idan ba ta niku da kyau ba za ta dinga dargajewa ba za ta yi da kyau ba.

5- Ki Nemi wani bowl daban ki fasa kwai a ciki

6- Sai ki sa whisk ki burka shi.
8- Ki kwashe wannan awarar ki zuba a cikin hadin kwan.
7- Ki sa maggi da gishiri da curry.

9- Bayan kin motsa zai yi haske kamar haka. Idan kwai bai ji ba ki kara guda daya

10- ki dora masa pan a wuta ki zuba mai
11- Sai ki sa silicon brush ki shafe ramin tandar da mai

12- ki debi kullun awarar ki dinga zubawa. Amma kada ki zuba da yawa saboda idan ya cika girma cikinsa ba zai nuna ba.
13- Sai ki sa murfi ki rufe. Amma babu matsala idan tandarki ba mai murfi ba ce.

14- Idan ya soyu sai ki juya dayan gefen.

15- Idan shi ma dayan ya soyu shi ke nan kin gama sai ki kwashe.

16- Shi ke nan sai a yi serving da dakakken yaji ko ketchup ko dai abin da mutum yake so.

Ku shiga Bakandamiya Shopping domin samun kyatattun kayan kitchen irin wanda na yi amfani da su