Uwargida ga yadda ake mango and banana smoothie cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi hudu da kuma steps biyu.
Abubuwan hadawa
- Mangoro biyu
- Ayaba guda uku
- Sugar cokali biyu
- Madarar gari cokaki hudu
Yadda ake hadawa
- Ki samu mangoro ki bare bawon ta ki yanka kanana ki sa a blender, ayaba itama ki bare ki yanka ki sata a blender.
- Ki sa ruwa rabin kofi, sugar da madarar gari ki yi blending na su. Za ki iya shanshi haka ko ki sa a fridge in ya yi sanyi ki sha. Tafi dadi idan ta danyi shanyi.
Alhamdulillah