Lentis soup ko adas shurba yana da dadi da amfani sosai ga jikin dan Adam, yana taimakawa wurin narkar da abinci, yasa ka ji cikinka sakayau. Yana da kuma auki sosai musamman idan kuka bi salon da na bi na yi nawa, dan haka Amarya da uwargida a shirya tsaf dan ganin yadda ake sarrafa shi.
Abubuwan hadawa
1. Adas
2. Dankalin Hausa kadan ko na Turawa
3. Tumatir
4. Albasa
5. Gishiri Da Dandano
Yadda ake hadawa
1. Da farko za ki fere dan madaidaicin dankalinki na hausa ko na turawa ko duka biyun, ki yanka su.
2. Sai ki yanka albasarki da dan tumatur dinki kadan.
3. Sai ki hada duka kayan da kika yanka wuri guda a cikin tukunya, ki kawo adas dinki ki zuba.

4. Sai ki zuba ruwanki dan madaidaici, ki saka dandano da na kayan kamshi.
5. Idan sun gama dahuwa luguf, sai a nika a a blender, a juye a bowl ko plate.
6. Za ki iya yi masa kwalliya da low fat cooking cream.
Wannan recipe an koyar da shine a Ramadan Recipes 2025 Webinar wanda Chef Shaima Alhussainy ta gabatar.