Ku koyi yadda ake lemun tsamiya cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi bakwai da kuma steps uku.
Abubuwan hadawa
- Tsamiya
- Kanunfari
- Bawon abarba
- Citta danya
- Borkono kanana kadan
- Sugar
- Ruwa
Yadda ake hadawa
- Ki samu tukunya ki zuba duk kayan hadin banda sugar ki bari ya tafasa sosai, sannan ki sauke ya huce, in ya huce sai ki tace.
- Ki samu wata tukunya daban ki sa sugar ki kunna wuta, amma wutar ki ya zamto ba ki cika ta ba, idan sugar ta narke ta zama brown sai ki sauke ki zuba ruwa akai ki juya. Sai ki zuba akan juice din tsamiyar.
- Ki sa a fridge in ya yi sanyi a sha.