Ku karanta ku koyi yadda ake lemun cucumber cikin steps biyu kacal. Domin yin wannan lemu, ana bukatar ingredients shida ne kawai.
Abubuwan Hadawa
- Cucumber
- Danyar citta
- Ruwan lemun tsami
- Flavour na butterscotch (ko duk flavour da ki ke dashi)
- Kankara
- Sugar
Yadda ake hadawa
- Ki samu cucumber ki wanke ta, ki yanka kanana da danyar citta ki sa a blender, sai ki rufe blender, ki nika su.
- Bayan ya yi sai ki tace ki sa suga, da ruwan lemun tsami, da flavour da kankara shikenan.
Karin bayani
- Za ki iya yanka cucumber slice ki zuba a ciki dan garnishing.