Lamb potato shurba soup ne da ake yinsa tsololo da naman karamar dabba irin rago, akuya haka, da kuma dankali.
Abubuwan hadawa
1. Nama
2. Dankali
3. Albasa
4. Tomato kadan
5. Kayan Kamshi
6. Dandano
Yadda ake hadawa
1. Da farko zaki wanke namanki ki ajiye a gefe.
2. Zaki fere dankali ki yankasu suma.
3. Ki yanka albasa dan kananu da tumatir shima kada ya wuce daya.
4. Za ki daura tukunya kisa mai kadan sai albasa sai tumatir kidan soya su, sai ki kawo nama kisa, ki kawo spices kisa, ki saka ruwa kaman za ki yi tafashen naman, kibarsa yai ta bararraka kaman awa biyu.
5. Sannan kisa dankali, ki bari su dahu luguf sosai-sosai , ana tabawa za kiga nama da dankalin sun fashe, ana dan diba da ruwan nan tsololo ana sha. Yana taimakawa matukar gaske ga hanjin mai azumi.
An koyar da wannan recipe na lamb potato shurba ne a Ramadan Recipes 2025 Webinar wanda Chef Shaima Alhussainy ta gabatar.