Yau za mu tattauna yadda ake kwallon doya (yam balls) a nan Bakandamiya Kitchen.
Abubuwan hadawa
- Doya
- Nikeken nama
- Attarugu 5
- Albasa 4
- Kwai 5
- Maggi 5
- Gishiri
- Kori
- Mai
Yadda ake hadawa
- Da farko zaki fere doyarki kiyanka ki wanke kisa atukunya ki dora a wuta da dan gishiri. Sai mu bashi mintuna samu doyarmu tanuna sosai.
- Idan ya nuna sai ki sauke ki kawo turmi mai tsafta ki daka doyarki ba dankan sakwara ba. Za ki yi sama-sama kawai. Sai ki kwashe idan ya yi ki zuba a roba mai fadi.
- Sai ki jajjaga attarugu da albasa ki zuba a kan doyarki. Sai ki juya sannan ki sa maggi da kori ki juya ya hadu sosai. Sai ki dinga dunkulawa kamar kwollo kina ajiyewa a tire.
- Idan kin gama sai ki kawo kwano mai kyau ki fasa kwai a ciki, sai ki dora kaskonki a wuta kisa mai. Idan ya yi zafi sai ki dinga dauko kwollon doyarki kina sawa a kwai kina kina sawa a wuta. Kar ki barshi a wuta ya jima.
- Idan ya yi sai ki kwashe. A zuba wa mai gida da yara. Na gode.