Skip to content

Yadda ake kwadon zogale

Share |
yadda ake kwadon zogale
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ga yadda ake kwadon zogale ku karanta ku koya. Wannan recipe ne mai saukin bin kuma da sauri, wadda za a hada cikin mintuna kalilan.

Abubuwan hadawa

  1. Zogale (dafaffe)
  2. Cucumber
  3. Garin kuli
  4. Tumatur
  5. Maggi
  6. Gishiri kadan
  7. Tattasai
  8. Albasa
  9. Man gyada
  10. Carrots

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko garin kuli ki daka tare da tarugu da albasa ki sa maggi iya dandano da zai miki, da gishiri sai ki daka ya daku ajiye a gefe.
  2. Dauko albasa, tattasai, cucumber, carrots, gyara ki wanke sosai da ruwan gishiri sai ki yanka su (irin yankan da ki ke so) ajiye a gefe.
  3. Dauko dafaffen zogalenki ki zuba garin kulinki (wanda ki ka daka tare da albasa, tarugu) sai ki cakuda sosai.
  4. Dauko su cucumber, carrots, tumatur, tattasai, albasa, (wanda ki ka yanka su) ki sa. Daga karshe sai ki dauko man gyada kadan ki yaryada a ciki. A ci dadi lafiya

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×