Skip to content

Yadda ake kwadon latas

Share |
Kwadon latas
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Karanta yadda ake kwadon latas Nigerian style.

Abubuwan hadawa

  1. Latas
  2. Karas
  3. Kwakwamba (Cucumber)
  4. Tarugu
  5. Tumatiri
  6. Tattasai
  7. Albasa
  8. Karago
  9. Man gyada
  10. Maggi star

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko latas naki ki gyara, ki wanke sai ki yanka shi, sannan karas ki cire dattin bayan, sai ki yi yanka da wuka, sai ki wanke sannan ki yanka su kwakwamba, da albasa, da tumatiri da tattasai , Sai ki ajiye a gefe.
  2. Ki dauko karagon da su Maggi, gishiri kadan da kayan kamshinki ki sa a turmi ki daka idan ya zama gari dauko albasa da tarugu ki yanka a ciki sai ki dake su a cikin garin karagonki.
  3. Sai ki dauko babban kwano Wanda zai isheki ki yi a ciki, ki dauko latas naki ki sa a ciki, ki kawo yajin karagon ki ki sa sai ki kawo karas, albasa, tattasai, kwakwamba ki sa, sannan sai ki juya a hankali.
  4. Daga karshe sai ki dan yaryada man gyada kadan. Sannan idan ki na so za ki iya matsa ruwan lemon tsami a ciki.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×