Skip to content

Yadda ake kunun tsamiya

Share |
yadda ake kunun tsamiya
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake kunun tsamiya mai ban sha’awa ga dadi ga kuma kyau. Ana bukatan steps tara ne domin hada wannan kunun tsamiyar.

Abubuwan hadawa

  1. Gero
  2. Tsamiya
  3. Sugar
  4. Kayan kamshi
  5. Borkono kadan

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko geron ki surfa ki bushe ko ki wanke shi sai ki shanya a rana ya bushe sai ki sa masa kayan kamshi da dan barkono ki watsa a ciki.
  2. Sai ki bayar akai miki nika. Da zarar an dawo miki da shi sai ki tankade garinki ki ajiye a gefe.
  3. Dauko tsamiyarki mai kyau ki wanke ta sannan ki sa mata ruwan zafi ki jika na dan wani lokaci. Ajiye a gefe.
  4. Daura tukunya akan wuta ki sa ruwa idan ruwan ya tafasa debo garin kadan a dan wani kwano, ki zuba garin kadan sai ki dubo ruwan zafi ki diga kadan sai ki murza shi har sai ya hade jikinsa.
  5. Sannan kina diban kadan kadan kina mulmulashi kina jefawa a cikin ruwan dake tafasa a kan wutan nan, sai ki barshi nadan wani lokaci.
  6. Daga nan sai ki diba garin kununki yadda zai ishe ki, ki kawo ruwan tsamiyan ki (ki tabbatar kin tace shi) ki zuba a kai ki dama. Idan kin ga ruwan tsamiyan ya yi kadan za ki iya kara ruwa a ciki yadan sake miki shi.
  7. Sai ki dauko tafashashshen ruwanki dake kan wuta (wanda ki ka jefa gaya a ciki) ki juye a kai. A take sai ki juya.
  8. Idan kin ga kaurin bai miki yadda ki ke so ba, za ki iya kara mai da shi cikin tukunya ki rage wuta, ki rika juyawa har sai ya yi miki kaurin da ki ke so.
  9. Sai ki sauke ki zuba a kofi ki sa sugar. A sha lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×