Ga yadda ake kunun madara, mu koya ‘yanuwa. wannan kunu ne da za a sha a kara har a sude kofi. Sai kun gwada ku zo ku ban labari!
Abubuwan hadawa
- Madara (ta gari)
- Couscous na kunu ko shinkafa(dafaffafiya)
- Filawa
- Citta da kaninfari
- Suga
Yanda ake hadawa
- Da farko ki dauko citta da kaninfari ki daka su sai ki jika da ruwa sannan ki tace, ajiye a gefe.
- Mataki na biyu ki dauko kwano ki tankade filawarki sai ki dama da ruwa (kaurin ya zama kamar kaurin kullin gasara)
- Na uku, ki dauko garin madaranki ki sa a kwano ki sa ruwa ki dama ta (iya ruwan da kika sa iya gardin kununki).
- Mataki na hudu, ki daura tukunya akan wuta ki sa ruwan madara ki ki rufe ta (amma ki na dubawa don karya zube idan ya tafaso) da zarar kinga yana haramar tafasowa sai ki kawo dafaffafen couscous na kunun ki ko dafaffafiyar shinkafa ki sa kina juyawa ahankali nadan wabi lokaci.
- Na biyar, bayan ya tafaso kashe wutanki, sai ki dauko kullin filawa ki na zubawa ki na juyawa a hankali har sai ya baki kaurin da ki ke so. Sai ki zuba tacacciyar citta da kaninfari kadan, sai suga yanda zai miki. A sha dadi lafiya.
Karin bayani
Idan kina so zaki iya gurza kwakwa a ciki.
Amfanin kashe wuta karin ki sa kullin filawa shi ne kunun ki zaiyi kyau ya yi smooth ba zaiyi burtsasi ba.