Skip to content

Yadda ake kunun gyada

Share |
yadda ake kunu gyada
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Uwargida ki duba yadda za ki yi kunun gyada mai ban sha’awa ga dadi ga kyau. Wannan kunun gyada baya bukatan wasu steps masu yawa sam.

Abubuwan hadawa

  1. Gyaɗa gwango biyu
  2. shinkafa
  3. lemun tsami ko tsami
  4. sugar

Yadda ake hadawa

  1. Aunty na da fari za ki wanke, ki gyara gyaɗar ki, ki jiƙa ta.
  2. Sai ki dauko shinkafar ki da ki ka gyara ki ka wanke, sai ki haɗa waje ɗaya da gyaɗarki.
  3. Daga nan sai ki ba da a markaɗo miki, bayan an kawo sai ki tace, ki ɗaura tukunya a wuta ki zuba ƙullun ki ringa juyawa da muciya har sai yayi kauri yanda ki ke so.

Sai ki sauke idan kin sauke sai ki matsa lemun tsami ko tsaminki, za ki ga ya yi fari tas ya yi kar kar kamar nono, se ki zuba suga sai sha.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake kunun gyada”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×