Ku koyi yadda ake kosai mai laushi ga dadi ga kuma kyau. Wannan kosai ana bukatan kayan hadi takwas ne domin hada ta.
Abubuwan hadawa
- Wake
- Albasa
- Tattasai
- Attarugu
- Gishiri
- Maggie
- Kwai
- Ruwa
Yadda ake hadawa
- Ki wanke wake ki gyara ki sa albasa, attarugu da tattasai ba dayawa ba sai a kai miki nika. Ki ce kar su cika miki ruwa. Bayan an kawo nikar, ki sa gishiri kadan da maggi (in ki ka sa maggi da yawa kullun ki zai yi baki. Kar maggin su wuce biyu in kullun na ki daidai misali ne).
- Sai ki sa ruwa kadan in kullun ya na da kauri.
- Ki fasa kwai ki buga kullun ki sosai za ki ga kullin tana canza color into a lighter one. Samun nika mai kyau da kuma bugu shine zai sa kosai ya yi kyau. Kwai kuma na kara masa laushi kuma in kina soyawa zakiga yana tashi mai kyau.
- Idan man ki ya yi zafi sai ki soya. Saboda idan man bai yi zafi ba kullun zai warwashe a ciki. A ci lafia.
Masha Allah