Ku koyi yadda ake jollof rice mai daddawa. Wannan jollof rice ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!
Abubuwan hadawa
- Tafasashshe shinkafa
- Kifi ko nama (ki dafa ki kidan soya)
- Daddawa
- Cray fish (ki nika)
- Ganyen Ugu dana water leave
- Man gyada
- Tarugu
- Albasa
- Tattasai (ki jajjaga)
- Kayan kamshi
- Maggi
- Gishiri kadan
Yadda ake hadawa
- Da farko za ki gyara ganyen ugu da na water leave ki yanka su ki wanke da gishiri ki tsanes u a matsami sai ki ajiye a gefe.
- Ki dauko tukunya, daura kan wuta ki sa mai ki yanka albasarki sai ki soya sama sama, sannan ki dauko jajjagen tarugunki ki sa a ciki ki juya ki soya sama sama shima, sai ki dauko daddawa kibsa, maggi (iya dandano da zai miki) gishiri kadan, cray fish, kayan kamshi ki sa su su ma. sai ki juya ki soya sama sama sannan ki dauko ruwan silalenki na kifi ki sa a ciki sai ki dan kara ruwan dumi (iya Wanda zai dafa miki shinkafa ki) sai ki rufe nadan wani lokaci ya yi ta tafasa
- Sai ki dauko shinkafa ki na zubawa a hankali ki na juyawa a hankali haka za ki yi har sai shinkafan ta kare. Sannan ki dauko kifi ko naman ki ki sake juya sai ki rufe tukunya ki kirib nadan wani lokaci.
- Daga karshe sai ki bude tukunya ki kawo ganyen ki zuba a ciki ki juya a hankali sai ki rufe tukunya nadan wani lokaci (amma ki tabbatar kin rage wuta sosai) sai ki sauke da zarar kin ji ruwan ya shanye kuma shinkafan ki ta nuna. A ci dadi lafiya.