Skip to content

Yadda ake jollof rice

Share |
Yadda ake jollof rice
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku karanta yadda ake jollof rice mai dadi da armashi.

Abubuwan hadawa

  1. Perboiled rice (tafasasshen shinkafa)
  2. Tumatiri
  3. Tarugu
  4. Karas
  5. Koren wake
  6. Dafaffafen kayan ciki
  7. Ruwan silalenki nama ko na kayan ciki
  8. Albasa
  9. Maggi (ya danganta da irin dandano ki)
  10. Kayan kamshi (Spices)
  11. Butter

Yadda ake hadawa

  1. Ki gyara karas na ki, ki cire dattin bayan, sai ki yanka shi, ki yanka koren wake. Sai ki sami baking powder ki sa akai ki kawo tafasashshe ruwan zafi ki sa a kai ki rufe nadan wani lokaci. Idan yayi laushi sai ki cire a ciki ruwan, ki sake wanke su da ruwa mai kyau ki tsane su a matsami sai ki ajiye a gefe.
  2. Dauko dafaffafen Kayan ciki nan (dama ya huce) ki yanka shi kanana kanana. Sai ki yanka albasa ki ajiye a gefe shi ma.
  3. Ki dauko tarugu da tumatir (amma tarugun yafi yawa) ki wanke, ki markada a blender (ko ki jajjaga).
  4. Ki daura tukunyanki a kan wuta ki sa butter ki kawo albasa ki sa, sai ki soya sama sama. Ki kawo kayan miyanki ki sa a ciki, ki soya sama sama shima, sai ki kawo kayan ciki ki sa a ciki ki dauko ruwan silalenki, maggi, Kayan kamshi da gishiri (iya yanda ki ke son dandano) sai ki juya a hankali ki kara ruwan zafi kadan inda zai iya dafa miki shinkafarki. Sai ki rufe tukunya har sai ya tafaso.
  5. Sannan ki dauko shinkafa ki zuba a ciki ki juya (idan baki so ta cabe ki rage ruwan hadinki a wani kwano daban sai ki zuba rabin shinkafa tare da albasa a cikin tukunya ki juya da Da mara, sai ki zuba ragowan shinkafa da ragowan ruwan hadinki tare da ragowan albasar ki juya da mara a hankali)
  6. Ki dauko leda ki rufe saman shinkafa (yin hakan yana hana tayi dahuwan gefe daya) ki rufe tukunya da marfi nadan wani lokaci har ruwan ciki ya shanye. Sai ki bude ki zuba karas naki da koren wake a ciki ki juya a hankali ki rufe tukunya sai ki rage wuta sosai. Ki barshi nadan wani lokaci sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×