Ku koyi yadda ake jollof na shinkafa da wake ga dadi ga kuma kyau. Wannan jollof na shikafa da wake na da saukin gaske wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Shinkafa
- Wake
- Kwai (dafaffe ki bare ki yanka kanana)
- Tarugu (ki jajjaga)
- Albasa (ki yanka)
- Tumatur mai kyau mai tauri (ki yanka kanana)
- Koren wake
- Peas
- Kayan kamshi
- Maggi
Yadda ake hadawa
- Ki daura tukunya kan wuta ki sa ruwa, ki gyara waken ki, idan ruwanki ya dauko tafasa ki zuba waken ki a ciki ki sa gishiri kadan, sai ki rufe.
- Idan ya fara tafasa ya dan yi laushi kadan, wanke shinkafar ki zuba a cikin waken ki rufe nadan wani lokacin har sai sunyi rabin nuna. Sai ki sauke ki kara ruwa ki tace ki tsane shi ki ajiye a gefe.
- Wanke tukunyar ki kara maida ta wuta ki sa mai ki yanka albasa ki soya sama sama sai ki kawo tarugunki ki sa a ciki ki juya.
- Ki kawo kayan kamshi, da maggi (iya dandanon da zai miki ki sa), sai ki kara ruwa (iya wanda zai karasa mi ki shinkafar ki. Sai ki rufe nadan wani lokacin har sai ya tafaso.
- Sai ki kawo shinkafa da waken ki zuba a ciki sannan ki juya a hankali ki ki rufe nadan wani lokacin har sai ruwan ya shanye sai ki kawo su peas, koren wake ki sa ki juya ki rufe sudan turara sai ki sauke ki kawo kwanki da tumatir ki sa ki juya a hankali sai ki zuba a plate.