Ku koyi yadda ake iloka mai dadi ga kuma kyau. Wannan iloka na da saukin hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya.
Abubuwan hadawa
- Condensed milk (oki gwangwani 1)
- Butter simas 1
- Garin madara cokali 2
Yadda ake hadawa
- Daura non stick pan naki akan wuta ki kawo butter ki sa ki bar shi har sai ya narke sai ki kawo madara ki zuba ki na juyawa a hankali har sai kinga ya fara kauri ya fara kalar brown sai ki kawo madarar garinki ki zuba a ciki sannan ki ci gaba da juyawa har sai kinga ya hade jikin sa ya yi brown sai ko sauke kidan bar shi ya sha iska sai ki fara mulmula shi irin shape da ki ke so. A ci dadi lafiya.