Mu koyi yadda ake icefish sauce ‘yanuwa. Wannan recipe ne mai sauki da kuma dadi ba kya bukatan bata lokaci wajen hada shi.
Abubuwan hadawa
- Kifi ice fish
- Albasa
- Tattasai da attarugu
- Tafarnuwa
- Man gyada
- Maggi
- Kayan kamshi
Yadda ake hadawa
- Bayan kin wanke kifinki ya tsane da kyau sai ki ajiye shi a gefe.
- Ki yanka albasanki sannan ki yi jajjagen tarugu da tattasai da tafarnuwa.
- Ki daura mai kan wuta, da ya yi zafi sai ki sa albasa ki kawo jajjage ki sa ki dan sa ruwa kadan ba mai yawa ba.
- Sai ki sa su maggi da kayan kamshi ki kawo kifinki ki zuba ki rufe ki maida wuta can kasa don ya samu ya dahu a hankali ba tare da ya farfashe ba.
- Akalla ki bari na minti biyar sai ki sauke.
Za ki iya ci da farar shinkafa ko taliya ko doya ko dankalin turawa ko ta Hausa ko plantain ko daima biredi da duk dai abinda za ki iya ci dashi.