Wannan hanya ce mai sauki wadda za ki iya yin homemade yoghurt yoghurt dinki a cikin gida. Sannan idan kin so har kasuwanci za ki iya farawa da shi. Kamar dai yadda kowa ya sani yoghurt ana sarrafa shi ne da madara, ruwan zafi, da kuma culture. To ga wadanda ma ba su sani ba, su biyo ni a cikin wannan recipe din zan warware maku zare da abawa. Idan ba ki taba gwadawa ba to za ki raba measurement dina gida biyu (Ya zama na 2 cups). Culture kuma 1/2 cup.
Abubuwan bukata
1- 4 cups powdered milk (I recommend lactorich for the perfect result)
2- 4 cups room temperature water
3- 4 cups boiling water (ruwa wanda yake kan tafasa)
4- 1 cup culture.
Yadda ake yi
1- Ki nemi babban bowl mai kyau ki auna madara 4 cups.

2- Sai ki zuba room temperature water (ruwa ba mai sanyi ba ba kuma mai zafi ba).

3- Ki jujjuya su su hade da kyau.

4- Ki kawo tafasasshen ruwa shi ma 4 cups din ki zuba ciki.

5- Za ki bar shi ne ya huce amma ba ya yi sanyi ba. Daidai yadda yatsarki dai za ta iya zama a ciki. Room temperature ke nan.

6- Sai ki samu plain yoghurt unsweetened mai kyau wanda yake da kauri (I recommend supercow ko kuma L&Z, ko dai wani mai kyau wanda aka rubuta DVS a jiki).

7- Bayan kin motsa da kyau sai ki tace.

8- ki juye a cikin airtight container sai ki nannade a cikin leda, ki nemi bargo ko wani abu mai nauyi ki lullube shi. Ko ki saka a cikin oven overnight ko akalla awa goma sha biyu.


9- Bayan kin fiddo shi za ki gan shi ya zama haka alamun yoghurt dinki ya yi ke nan.

10- Ki zuba flavor da sugar yadda kike so. Shi ke nan an gama homemade yoghurt.

Za ku iya samun measument cups da sauran kayayakin a cikin bakandamiya shopping.