Ku koyi yadda ake hadin shinkafa ta musamman. Wannan hadin shinkafa ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya!
Abubuwan hadawa
- Shinkafa
- Kayan kamshi
- kwai
- Albasa mai lawashi
- Koriyar tattasai
- Peas
- Karas
- Albasa
- Bay leaves
- Maggi da gishiri
- Man gyada
- Nikakkiyar nama
- Curry
Yadda ake hadawa
1. Da farko za ki fara dafa shinkafarki da curry ki ajiye a gefe.
2. Ki kada kwai ki soya ki dagargaza ki ajiye a gefe.
3. Sai ki daura mai ki kawo albasa mai lawashi ki zuba da koriyar tattasai da nikakkiyar nama da maggi da kayan kamshi ki soye duka ki sa kayan lambunki duka.
4. Sannan sai ki dauko dafaffiyar shinkafa ki sa a ciki ki cakude ko ina yaji sai ki kawo kwan ki zuba ki rufe ki bari ya turara.
Shikenan sai rabawa a ci.