A yau za mu ko yi yadda ake hadin dambun nama.
Abubuwan hadawa
- Nama mara kitse kilo
- Attarugu
- Maggi
- Albasa
- Gishiri
- Tafarnuwa
- Cittah
- Mangyada
- Kori
Yadda ake hadawa
- Da farko zaki wanke namanki ki sa albasa da maggi ki dora a wuta ki tafasa ya nuna sosai.
- Idan yayi sai ki sauke ki kawo turminki mai kyau ki daka namanki ya daku sai ki kwashe.
- Sai ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa da cittah ki zuba akan dakekken namanki kisa, sannan ki sa maggi da kori ki juya sosai komai ya hadu.
- Idan yayi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mangyada ki zuba namanki ki yi ta juyawa har sai yayi yanda kike bukata.
- Idan yayi sai ki sauke ki juye a wani abu mai kyau.
Na gode.
Photo Credit: Funke Koleosho