Skip to content

Yadda ake hada zobo cikin sauki

yadda ake hada zobo cikin sauki
3.9
(7)

Ku koyi yadda ake hada zobo cikin sauki. Wannan hadin zobo yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Zobo
  2. Abarba  (rabi – 1/2)
  3. Cittah danya
  4. Kanunfari
  5. Kukumba
  6. Sukari
  7. Abin kamshi (flavour)

Yadda ake hadawa

  1. Da farko sai ki sa zobonki a tukunya da ruwa, kuma ki sa kanunfari da cittah
  2. Sai ki fere abarbanki da kukumba, ki yanka kanana, sai ki zuba a bilenda ki markada,  sai ki gurza cittah
  3. Sannan sai ki tace da zobonki, kisa sugarki da abin kamshi ki juya sosai, saiki dandana kiji in komai yayi daidai.
  4. Sai ki saka kankara ko kuwa ki sanya firinji don ya yi sanyi

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×