Ga yadda ake strawberry smoothie, mu koya ‘yanuwa. Wannan smoothie ne mai rai da motsi wadda kowa zai so kuma ga sauki hadawa.
Abubuwan hadawa
- Mangoro
- Yogat (yoghurt)
- Strawberry (faraula)
- Suga
Yadda ake hadawa
- Ki wanke managoro ki yayyanka kanana sai ki zuba yoghurt a blender ki nika da suga ki ajiye a gefe.
- Hakanan shima strawberry ki wanke shi ki sa yoghurt ki nika su lukui da suga shima ki ajiye a gefe.
Yadda za ki zuba a kofi ya ba da sama daban kasa daban
- Ki sami kofinki na gilashi me kyau ki zuba niqaqqiyar mangoron rabi dai dai sai ki tsaya.
- Sai ki dauko nikakkiyar strawberry ki na diba da cokali a hankali kina zubawa kadan kadan har ya cike kofi din.
- A hankali za ki rika zubawa dan kada ya cakude da cokali.