Skip to content

Yadda ake gugguru (popcorn)

Share |
yadda ake gugguru (popcorn)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Uwargida ki koyi yadda ake gugguru (popcorn). Wannan popcorn yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Masarar gugguru (popping corn)
  2. Butter ko mai
  3. Sugar
  4. Madarar gari

Yadda ake hadawa

  1. Ki sami tukunyarki mai marfi ki daura kan wuta sai ki zuba mai ko butter a ciki (Dan daidai mai din). Ki barshi a kan wuta ya yi zafi idan kuma butter ce ki zubata har sai ta narke ta yi zafi.
  2. Sai ki zuba masarar ki a ciki ki rufe tukunyar ki. Za ki ga ya fara fashewa yana tsalle (karki bude marfin tukunya) da zarar kinji ya fara fashewa sai kina girgiza tukunya (hakan zai hana shi konewa ya yi baki baki) haka za ki ta girgiza tukunyarki har sai kinji masarar ki baya karar fashewa.
  3. Sai ki rage wuta ki bude ki yaryada sugar (iya zakin da zai miki).
  4. Sai ki juya ki sauke sannan ki zuba madarar garin ki a kai.
  5. Sai ki kwashe ki sa a roba mai marfi wanda iska ba zai shiga ba a ci dadi lafiya

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake gugguru (popcorn)”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×