Skip to content

Yadda ake grilled sandwich

Share |
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake grilled sandwich.

Abubuwan hadawa

 1. Biredi mai yanka
 2. Soyayyen plantain(agada)
 3. Kwai
 4. Nama (ki dafa, ki daka)
 5. Tarugu (ki jajjaga ko ki yanka)
 6. Koren wake (ki yanka)
 7. Karas (ki yanka)
 8. Kabeji (ki yanka)
 9. Maggi
 10. Gishiri
 11. Butter
 12. Abun gashi (manual sandwich grill)

Yadda ake hadawa

 1. Da farko ki daura kasko akan wuta ki sa mai ko butter kadan ki kawo dakakken namanki ki sa sannan ki kawo tarugu, albasa da ruwa kadan (kamar cokali hudu) ki sa ki juya sai ki sa maggi (iya dandanon da zai miki) ki sa ki juya gishiri ki sa kadan da kayan kamshi, ki juya sai ki rufe nadan wani lokacin (Har sai ruwan ciki ya shanye).
 2. Dauko kabeji, karas, koren wake (wanda ki ka yanka su) ki sa ki juya ki rufe nadan wani lokaci ya turaru, bayan ya turaru sai ki sauke ki ajiye a gefe.
 3. Ki dauko abun gashinki, ki sa biredin mai yanka daya a ciki sannan ki kawo hadin naman ki ki sa ki kawo soyayyen agada (plantain) ki sa kamar yanka 3-4 ki daura akan hadin naman (wanda ki ka riga ki ka sa).
 4. Sai ki dauko wani biredi mai yanka ki rufa akan hadin ki sai ki rufe abun gashinki kirib (shi da kansa za ki ga ya yanke gefe gefen ma) idan kuma bai gama yankewa ba sai ki sa hannu ki cire gefe gefen.
 5. Ki kunna gas, stove ko gaushi (za ki iya gashin akan ko wanne) ki daura abun gashin biredin ki akai ki gasa nadan mintuna sai ki juya dayan gefen shima ki gasa har sai ya gasu sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

Za a iya dubaYadda ake gugguru pop corn da yadda ake beef samosa, meat pie, ko spring roll filling da ma wasu girke-girke da dama.

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading